Jakadan Nijeriya A Saudiya Ya Yi Watsi Da Zargin Yana Da Hannu A Fataucin Mata


Jakadan Nijeriya a Sa’udiyya ya musanta zargin cewa yana da hannu a safarar mata daga Nijeriya zuwa Sa’udiyyan inda ake bautar da mata kamar bayi.

Jakadan Nijeriya a Sa’udiyya, Isa Dodo ya nesanta kansa da zargin cewa yana da hannu wajen kai mata da sauran mutane Sa’udiyya don ayyukan hidima, inda sukan kare cikin wahala da nadama.

Isa Dodo wanda aka zanta da shi daga Riyadh, na maida martani ne ga labarin da wani dandalin yanar gizo SECRET REPORTERS wanda ya yada da nuna jakadan na da hannu a wannan lamari da ya yi kama da fataucin bil adama.

Dodo ya ce, kullum shi da jami’an sa na kara kaimi don bin kadun ‘yan Nijeriya da suka samu matsala, idan ma suna hannun ‘yan sanda ko gidan yari ne.

Ga alhazan da za su fara shiga Sa’udiyya a watan nan, Dodo ya ce su lura da tashin farashin kaya har ma da abinci don haka su yi tsimi da tanadi.

Kwanakin baya an samu mata mazauna Sa’udiyya da ke kokawa kan jefa su cikin ukuba da a ke yi a kasar.

Wani direba da ya nemi tafiya bai samu ba don wata jinya da ya ke da ita, matar sa ta samu tafiya shekaru biyu shiru ta ki dawowa don ma har ta turo an saya ma ta gida a nan Nijeriya ta bar mijin na sallallami.

Wasu kungiyoyin Islama da a ka zarga da hannu a wannan jigila sun yi watsi da zargin da hakan ya sanya kamfanonin kai mutane Sa’udiyya su ka fito karara su ka ce su ke wannan aiki kuma su na da rejista da duk hukumomin da su ka dace.


Like it? Share with your friends!

1
95 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like