Jakadan Najeriya a Iraqi ya rasu


Jakadan na Najeriya a kasar Jordan da Iraqi Mallam Haruna Ungoggo ya rasu ya nada shekaru 75.

Jakadan ya rasu ne a asibitin Garki dake Abuja bayan ya shafe kwanaki biyar yana jiya.

Wasu majiyoyi dake da kusanci da iyalan marigayin sun bayyana cewa za a yi jana’izarsa ranar Litinin a Kano.

A ranar 14 ga watan Oktoban shekarar 2016 ne shugaban kasa Muhammad Buhari ya zabe shi domin ya zama jakada.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 53

You may also like