Jagororin jam’iyar PDP a Kano sun gudanar da wani taro a Abuja


Jagororin jam’iyar PDP na jihar Kano sun yi wata ganawa a gidan ɗaya daga cikin jagororin jam’iyar.

Ganawar ta gudana ne a gidan Ambasada Aminu Bashir Wali dake birnin tarayya Abuja.

Jagororin sun tattauna akan makomar jam’iyar PDP a jihar da kuma batun zaben shekarar 2019.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau sanata Bello Hayatu Gwarzo da kuma shugaban jam’iyar na jihar sanata Mas’ud El-jibril Doguwa.

Biyo bayan komawa jam’iyar PDP da tsohon gwamna Kwankwaso ya yi mutane da dama sun nuna shakku kan dunkulewar manyan yan siyasar guri guda.

Sai dai ya zuwa yanzu alamu na nuni da cewa yansiyar za su bawa marada kunya ganin yadda suka dunkule wuri guda.


Like it? Share with your friends!

-1
112 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like