Jagoran juyin mulkin kasar Sudan ya sauka daga mukaminsa


Awad Ibn Auf, ministan tsaron kasar Sudan wanda ya jagoranci juyin mulkin da ya kai ga hanbarar da gwamnatin shugaba ,Omar Albashir ya sauka daga kan mukaminsa.

Ya sanar da matakin sauka daga mukaminsa ranar Juma’a a wani jawabi da aka yada ta kafafen yada labarai na kasar.

A jawabinsa ya ce a yanzu wani sabon janar na soja shi zai cigaba da mulkin ƙasar.

Bayan tilastawa shugaba Albashir sauka daga mukaminsa na shugaban kasa, Auf ya sanar da cewa sojoji za su cigaba da jagorancin ragamar mulkin kasar na tsawon shekaru biyu kafin a gudanar da zabe.

Amma masu zanga-zangar wadanda tun da fari suka bukaci murabus din Albashir sun cigaba da matsin lamba kan sojojin su kauce daga kan mulkin kasar.

Sun ki yarda sun bar kan tituna inda suke zargin cewa jagororin juyin mulkin makusantan tsohon shugaban kasar ne.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like