Iyalan tsohon gwamnan Adamawa Saleh Michika sun koka kan yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da shi


Awanni kadan bayan mutuwar, Abubakar Saleh Michika, gwamnan farar hula na farko na jihar Adamawa iyalinsa sun zargi gwamnatin jihar da yin watsi da shi.

A wata tattaunawa da jaridar Daily Trust dansa, Abdulrashid Saleh Michika ya ce gwamnati taki ta saki kudin fanshonsa a matsayinsa na tsohon gwamna ko kuma ta dauki nauyin kula da lafiyarsa kamar yadda doka tace a yi masa.

Ya koka cewa ko lokacin da kwararrun likitoci dake Cibiyar Kula Da Lafiya Ta Tarayya dake Yola suka sanar da gwamna Muhammad Jibrilla Bindow cewa basu da cikakkun kayayyakin aiki da ake bukata domin kula da halin da tsohon gwamnan ke ciki inda suka nemi a kawo jirgin daukar marasa lafiya domin kai shi asibiti dake da kayan aiki amma gwamnan ya gaza basu ansa.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar tana rike da kudadensa na fansho da ya kai miliyan  ₦400 duk da alkawarin biya da gwamnan ya yi. amma a karshe sai gwamnatin ta rage kudin fanshonsa ya zuwa ₦300,000 kacal.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like