Makwanni 2 bayan bullar rahotannin da ke bayyana cewa shugaban kungiyar Boko Haram ya mutu, kungiyar mayakan IS ta yankin Afirka ta yamma wato ISWAP, ta tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ya sami wani sautin murya daga hannun da ya ke samun sakwannin da suka gabata na kungiyar, inda shugaban ISWAP din Abu Musab Al-Barnawi, ya ke tabbatar da cewa Shekau ya kashe kan sa ne ta hanyar tayar da bam da ke jikinsa.

Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram

Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram

A cikin sakon muryar, Al-Barnawi ya ce ISWAP ta aike da mayakanta a dajin Sambisa inda suka kai farmaki ga shugaban na Boko Haram, inda “daga nan ya sami arcewa ya buya a cikin jeji tsawon kwanaki 5.”

Al-Barnawi ya ci gaba da cewa “mayakan mu sun ci gaba da farautar sa, suka kuma gano shi, kana suka nemi da ya tuba ya mika wuya, amma kuma sai ya ki, a maimakon haka ya kashe kan sa.”

Shugaban na ISWAP ya ce “Shekau ya zabi azaba da wulakancin lahira akan na duniya, shi yasa ya kashe kan sa nan take, ta hanyar tarwatsa kan sa da bam.”

“Mun yi farin ciki da haka” in ji muryar ta Al-Barnawi, “Shekau mutum ne da ya aikata munanan ayukan ta’addanci.”

Har kawo yanzu dai kungiyar Boko Haram ba ta ce komai ba a hukumance dangane da mutuwar shugaban na ta, wanda ya kwashe shekaru fiye da 10 yana haddasa ayukan ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Ita kuwa rundunar sojin Najeriya, ta ce tana ci gaba da bincike akan ikirarin mutuwar ta Shekau.

Rundunar Sojojin Nijeria Sun Sha Alwashin Cigaba Da Farautar Yan Boko Haram

Rundunar Sojojin Nijeria Sun Sha Alwashin Cigaba Da Farautar Yan Boko Haram

Wannan kuma ba shi ne karo na farko da ake ba da rahoton mutuwar shugaban na Boko Haram ba tsawon shekaru 12, amma daga bisani kuma ya bayyana a sakon bidiyo yana karyatawa.

Ayukan kungiyar ta Boko Haram sun kara kamari ne bayan sace dalibai 270 a garin Chibok a shekarar 2014, lamarin da ya ja hankalin duniya baki daya, har aka shiga gangamin neman kubutar da daliban.

Da farko kuma ISWAP sashe ne na kungiyar ta Boko Haram, amma kuma daga bisani a shekarar 2016 suka balle tare da yin mubayi’a ga kungiyar IS.

Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito masu fashin baki na bayyana ra’ayin cewa mutuwar ta Shekau kan iya kawo karshen takaddama tsakanin kungiyoyin biyu na ISWAP da Boko Haram, wanda kuma zai baiwa ISWAP din damar mamaye Boko Haram, domin ta kara kwari da mamayar ta a Arewa maso gabas.