Ishaku ya sanya hannu kan dokar hukuncin kan masu garkuwa da mutane


Gwamnan jihar Taraba,Darius Ishaku ya sanya hannu kan kudirin dokar da ya amince a zartar da hukuncin kisa da kuma daurin rai-rai ga masu garkuwa da mutane.

Bala Dan Abu mai taimakawa gwamnan kan kafafen yada labarai shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ishaku ya rattaba hannu kan kudirin dokar ranar Laraba a Jalingo bayan da majalisar dokokin jihar ta zartar da kudirin bayan anyi masa karatu na uku.

A ranar Talata ne majalisar dokokin tayi gyara kan dokar shekarar 2010 wacce ta hana yin garkuwa da kuma sace mutane inda aka saka hukuncin kisa da kuma daurin rai-rai.

A karkashin sabuwar dokar duk wanda aka samu da laifin sacewa ko kuma yin garkuwa da wani mutum to zai fuskanci hukuncin kisa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like