Ishaku ya lashe zaben gwamnan Taraba


Hukumar zabe mai zaman kanta ta ayyana gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Shehu Adamu Iya wanda ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zabe dake Jalingo ya ayyana Ishaku a matsayin wanda ya lashe bayan da ya samu kuri’u mafi yawa.

Ishaku ya samu kuri’u 520433.

Har ila yau jami’in tattara sakamakon sakamakon ya ce dan takarar gwamna na jam’iyar APC, Alhaji Sani Abubakar Danladi shine yazo na biyu a zaɓen da kuri’u 362,735.

Gwamnan ya tsaya takara ne a karo na biyu karkashin jam’iyar adawa ta PDP.


Like it? Share with your friends!

2
55 shares, 2 points

Comments 2

Your email address will not be published.

  1. Allah ya isa mana domin ba’ayi zabe ingaatacce na adalciba A taraba shi kansa ya San ba ayinsa saboda baiyi komaiba in banda babbancin qabilanci da yake nunawa Allah yasaka mana PMB Allah ya baka ikon tabbatar da adalci wannan qasa Nigeria

You may also like