Hukumar da ke aikin sarrafa makamashin nukiliya ta kasar Iran, IAEO, ta sanar a ranar Lahadi cewa an kai wa cibiyar nukiliyarta ta Natanz harin ta’addanci.

Shugaban hukumar da ke sarrafa makamashin nukiliyar Ali Akbar Salehi, duk da cewa bai bayyana sunan kasar da Iran ke zargi da kai mata harin ba, amma ya ce makiyan Iran ne da ke son ganin sun hana ta bunkasa ta fuskar masana’antu da siyasa suka kai mata harin. 

Harin na ranar Lahadi, wanda ya kai Iran din ga yin barazanar iya kai hari na ramuwar gayya a kan Isra’ila, na iya kawo nakasu ga kokarin manyan kasashen duniya na dawo da yarjejeniyar da ta kama hanyar wargajewa game da makamashin na Iran.

Ana kallon in har ta tabbata Isra’ilar ce ta kai harin, toh la budda dangantaka za ta kara dagulewa a tsakanin kasashen biyu.