Iraki: Gobara ta halaka majinyatan corona 82 | Labarai | DWDa dama daga cikin wadanda gobarar ta rutsa da su na masu dauke da cutar corona ne da suke kan na’urar da ke taimakawa marasa lafiya numfashi. An dai alakanta tashin gobara daga yoyon  tukwanan iskar gas.

Ma’aikatar lafiyar kasar ta ce ko baya ga wadanda suka kone kurmus a gobarar wasu sun mutu a sakamakon hayakin da suka shaka yayin da wasu kuma suka mutu sanadin cire su da aka yi daga na’urar ventilator da ke taimakawa mutum wajen yin numfashi.

Tuni dai Firaminista Mustafa al-Kadhemi ya sanar da dakatar da ministan lafiyar kasar bayan wannan mumunar gobara, lamarin da ke ci gaba da jan hankulan al’umma da ke bukatar korar ministan daga aiki maimakon dakatar da shi na wani lokaci.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg