INEC taki yarda da janyewar Ezekweseli daga takarar shugaban kasa


Hukumar zabe ta kasa INEC tace lokaci ya kure da kowane dantakara zai iya janyewa daga tsayawa takara a zabe mai zuwa.

INEC ta bayyana haka ne lokacin da take mayar da martani kan janyewar da mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyar ACPN, Oby Ezekweseli ta yi.

Ezekweseli ta sanar da janyewar tata ranar Alhamis inda tace tana son bayar da damar hada wata gamayya da zata kalubalanci jam’iyun APC da PDP.

Amma da yake mayar da martani cikin wata sanarwa babban jami’in yada labarai na shugaban hukumar, Rotimi Oyekanmi ya ce ranar 17 ga watan Nuwamba itace ranar karshe ta janyewa ko kuma sauya dantakara.

Sanarwar tace: ” ba zai yiyuwa ba kowane dantakarar shugaban kasa ya janye daga shiga zabe ba a yanzu.La’akari da jadawali da kuma tsarukan babban zaben 2019 rana ta karshe ta janyewar dantakara ko kuma jam’iya ta maye gurbinsa da wani itace ranar 17 ga watan Nuwamba ga yan takarar shugaban kasa da kuma na majalisun tarayya,”

“Wa’adin da Ezekweseli ko kuma wani dake takara da ya fado wancan rukuni na janyewa ko kuma a maye gurbinsa ya wuce.”


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like