Hukumar zabe ta kasa INEC ta tsawaita wa’adin karbar katin zabe da kwanaki uku ya zuwa ranar litinin.

Shugaban hukumar, Mahmoud Yakubu shine ya bayyana haka yayin wata ganawa da ya gudanar da kwamishinonin zabe na jihohi ranar Juma’a a Abuja.

Tunda fari an saka ranar Juma’a a matsayin ranar karshe ta karbar rijistar zaben.

Amma Yakubu ya ce an tsawaita wa’adin ya zuwa ranar 11 ga watan Faburairu domin tabbatar da cewa ba a hana wani wanda aka yiwa rijista ba yancinsa na kada kuri’a.

Ya ce yanzu za a rika karbar katin daga karfe 9 na safe zuwa 6 na kowace rana.