INEC ta tabbatar da sunan Tambuwal a matsayin dantakarar gwamna a jam’iyar PDP


Hukumar zabe ta kasa,INEC ta tabbatar da Aminu Waziri Tambuwal a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyar PDP a zaben shekarar 2019.

Festus Okoye, kwamishinan hukumar na kasa dake kula da bangaren yada labarai da kuma wayar da kan masu kada kuri’a shine ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da ya yi da jaridar New Telegraph.

Tun da fari hukumar zaben ta gaza saka sunan Tambuwal cikin jerin sunayen yan takarar gwamnan jihar Sokoto da ta wallafa a kwanakin baya.

A cikin jerin sunayen an bayyana Mannir Daniya a matsayin dantakarar gwamna a karkashin jam’iyar PDP.

Amma kuma a yanzu an tabbatar da sunan Tambuwal a matsayin dantakara ya yin da Mannir Dan’iya zai kasance mataimakin sa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like