INEC Ta Soke Zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa Dake Jihar Bauchi


Labarin da ke fitowa da duminta daga cikin ofishin INEC da ke Bauchi, na tabbatar da cewar babban jami’in tattara sakamakon zaven gwamnan jihar Bauchi Farfesa Kyary Muhammad mukaddashin shugaban jami’ar Futi da ke Yola, ya soke zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar ta Bauchi.

Farfesan ya soke sakamakon zaben ne bayan da muhawara mai karfi ta barke a tsakanin wakilan jam’iyyun da suka hada da APC, PDP, PRP, jimkadan bayan da jami’ar tattara sakamakon wannan mazabar ta bayyana kalubalen da suka fuskanta a lokacin gudanar da zaben da lokacin tattara sakamakon zaben.

Misis Dominion Anosike ita ce jami’ar tattara sakamakon zaben mazabar karamar hukumar Tafawa Balewa, ta shaida a filin amsar sakamakon cewar an tursasa mata wajen shigar da ababen da basu dace ba a yayin da ake tattara sakamakon zaben wannan karamar hukumar.

Tana mai shaida cewar an samu barazana sosai da kuma fuskantar mummunar kalubale na kai mata farkamaki, inda ta shaida cewar hatta sakamakon zaben da ta zo da shi, ta zo da shi ne ba a takardar da ya dace a kawo sakamakon zaben ba, ta ce, hakan ya faru ne kuma a sakamakon farmakin da aka kai mata, don haka ne ta ce sakamakonta akwai matsala a ciki.

Jami’in jam’iyyar APC a wajen, ya shaida cewar sakamakon zaben na bogi ne wanda aka tsara a gefe, don haka ne ya buqaci shugaban da ke amsar sakamakon zaben ya yi nazarin sakamakon cikin hanzari.

Wakilin jam’iyyar PDP shi kansa bai yi musun matsala ba, inda ma ya ce a dokance yake idan da an samu artabu da kai farmaki a wajen rumfunar zabe har aka tabbatar da fada shine za a soke zaben, ya dai nemi kada a soke zaben karamar hukumar gaba daya, ya ce amma muddin har aka zo wajen bayar da sakamakon zabe ba tare da matsala ba shi kenan.

Nan take dai shugaban da ke tattara sakamakon zaben ya sanar da soke zaben a bisa rashin sahihancin zaben.


Like it? Share with your friends!

-2
88 shares, -2 points

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Write a comment *agaskia wannan jamiar hukumar inec Allah yasaka mata da alkhairi da shi shugaban zaben gaba daya, saboda garin tafawa balewa garine me cike matsalolin kabilanci dakuma addini’ danhaka abi doka azauna lafiya, daga safiyanu bello kwabtin rimi town tafawa balewa LGA Bauchi state mazaunin garin kano ta dabo,,,

You may also like