INEC Ta Samu Gwamnan Jihar Kogi Da Laifin Yin Rijistar Zabe Sau Biyu 


Hukumar zabe ta kasa INEC ta tabbatar da cewa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, yayi rijistar yin zabe har sau biyu.

Solomon Soyebi Kwamishinan hukumar na kasa mai kula da sadarwa da kuma ilimantar da masu kada kuri’a, ya bayyana haka jiya Alhamis a Abuja, inda yaci alwashin hukunta ma’aikacin hukumar da yayi gwamnan rijistar a karo na biyu. 

Yace bayan da Bello yayi rijistar sa ta farko a Abuja,a ranar 30 ga watan janerun 2011, ya sake yin ta biyu a ranar 23 ga watan Mayun wannan shekara a gidan gwamnati dake Lokoja. 

Soyebi yace anyi rijistar ba a cibiyar da hukumar ta ware ba don cigaba da yiwa masu zabe rijista.

Wata kungiyar farar hula ce ta bankado yadda gwamnan yayi rijistar sau biyu kuma tayi barazanar kai shi gaban kotu.

Hukumar zaben ta kasa ta ware ofisoshinta da suke kananan hukumomi 774 na kasarnan a matsayin cibiyoyin da za’a cigaba da yiwa Jama’a rijistar. 

Yin rijista sau biyu da kuma yi masa da akayi a gidan gwamnatin jihar duka laifi ne da ya sabawa doka a cewar Soyebi. 

Tuni hukumar ta INEC ta soke rijistar gwamnan da yayi a karo na biyu.
Sai dai duk da gwamnan ya saba doka, hukumar baza ta iya hukunta shiba saboda  kariyar da tsarin mulki ya bashi daga gurfana a gaban Shari’a.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like