Inda Ranka : Wani Matashi ya kai karar iyayensa saboda sun haife shi babu izinin sa


Wani matashi mai shekaru 27 da ake kira Raphael Samuel, dan asalin kasar Indiya, ya kai karar iyayensa kotu saboda sun haife shi ba tare da amincewar sa ba.

Raphael ya bayyana cewar yana matukar kaunar iyayen sa amma duk da haka ya gaza fahimtar banbancin da ke tsakanin haihuwar sa da bautar da shi ko yin garkuwa da shi, ya na mai fadin cewar bai ga banbanci tsakanin su ba tun da dukkan su na faruwa ne ba tare da amincewar mutum ba.

Dan asalin birnin Mumbai, Rapahael ya ce rashin adalci ne ga iyaye su haifi mutum don kawai son jin dadin su ko samun farin ciki ba tare da yin la’akari da irin wuyar da zai sha a rayuwar duniya ba.

A wata hira da aka yi da shi, Raphael ya ce; “Ina son iyaye na kuma akwai jituwa da shakuwa tsakani na da su, amma sun haife ni ne domin jin dadi da farin cikin su .

“Duk da rayuwata ba a cikin wani kunci ta ke ba, amma ban ga dalilin da zai sa a haifi mutum don kawai ya zo duniya ya sha wahalar karatu da neman aiki ba, musamman ganin cewar babu amince wa ko yardar sa kafin faruwar hakan .”


Like it? Share with your friends!

3
100 shares, 3 points

Comments 7

Your email address will not be published.

You may also like