INDA RANKA: KABILAR HIMBA: Mutanen Da Ba Su Taba Yin Wanka Ba A Rayuwarsu


Kabilar Himba, wasu mutane ne da suke zaune a kudancin Afirka a wata kasa mai suna Namibia. Namibiya kayataccen gari ne mai tsaunuka da namun daji kala-kala. Wannan shi ya sa mutane masu yawon buɗe ido sukan zo daga garuruwa. Babban dalilin shaharar wannan kabila shi ne, wasu bakin al’du da suke da su waɗanda ba kowa ne yake da su ba. Da farko dai su mutanen nan suna zaune a arewcin garin Namibia.

Kuma sun killace kansu daga barin hulɗa da mutanen da suke wajen garinsu. Amma kuma an ce suna da karrama baki har ma idan bako kwana zai yi ma sukan ba wa bako aron matansu. Sannan kuma suna da haɗin gwiwa da kabilun da suke makwabtaka da su wajen fatattakar duk wanda zai kawo suka a kan waɗannan al’adun nasu.

Babban dalilin da ya sa Mutanen Himba, ba sa wanka, shi ne: Da farko akwai karancin ruwa matuka da suke da shi saboda yadda yanayin garin nasu yake sahara ne. Sannan kuma a al’adarsu wanka ya saɓa wa al’ada. Hanyar da suke amfani da ita wajen tsaftace jikinsu ita ce: za su sami garwashin wuta su zuba shi a kwanon da aka cika da busassun ganyaye da hakukuwa, ko sassake.

Sai mutum ya nemi bargo ya lulluɓa ya turara jikinsa har sai hayakin ya ratsa jikinsa ya yi zufa sannan zai fita. Har yau a haka suke. Babban ɓacin ransu ka nemi ka canza musu wannan al’ada tasu da suka gada kaka da kakanni. Gwamnatocin Iceland da Norway sun yi iya kokarinsu amma ba su yi nasara ba.


Like it? Share with your friends!

-1
98 shares, -1 points

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like