Ina Ma’abota Daukan Hoton Selfie: Attajiri Ya Rasa Ransa A Yayin Daukan Hoton Selfie


Wani babban attajiri a kasar China, mai kamfani mafi girma na 4 na kasar HNA, biloniya Vang Cian ya fado kasa yayin daukar selfie kan wata katanga mai tsawo a kasar Faransa.

Vang shugaban hadakar kamfanonin HNA, wanda ke da shekaru 57 da haifuwa ya rasa ransa, bayan da ya fado daga wata katanga mai mita 15, a lokacin da yake kokarin daukar selfie a kauyen Bonnieux na yankin Provence da ke kudu maso gabashin Faransa.

An sanar da cewa attajiri Vang ya kai ziyara Faransa da nufin kashe kawarkwatar idanu.


Like it? Share with your friends!

-1
101 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like