Ina Da Tabbacin Zan Yi Nasara a Wannan Zabe – Atiku Abubakar


fb_img_1550688080987934430374.jpg

 

Dan takaran shugaban kasa a jam’iyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana tabbacinsa na lashe zabe da aka gudanar a jiya Asabar duba da sakamakon da ya gani a wasu mazabu tun daga jiya.

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa da ya ke karawa da shugaban kasa da ke kan mulki, Muhammadu Buhari, ya bayyana haka ne a jawabi da jami’in yada labarunsa, Phrank Shuaibu ya fitar a jiya. Atiku ya gode wa al’uma bisa yadda su ka yi dafifin fito suka zabeshi.

 

Daga karshe ya bukaci magoya bayansa da su sake zuba ido tare da tabbatar da cewa an kirga kuri’unsu a gaban idanunsu a mazabunsu domin tabbatar da cewa jam’iyar APC ba ta yi musu magudi ba.


Like it? Share with your friends!

-2
80 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like