ILLOLI GOMA DA MADIGO KE HADDASAWA GA JIKI


Madigo wanda a turance ake kira da lesbianism yana nufin saduwa ta hanyar gogayya tsakanin mace da mace ta amfani da halittarsu dan kauda sha’awar juna.Idan wannan ya kasance a tsakanin namiji da namiji to ya koma luwadi kenan.Waiyazu billah!

Neman jinsi ya faro ne tun daga zamanin Annabi Lud (a.s) wanda tarihi ya nuna cewa shaidan ne ya zo a cikin siffar ‘yan adam ya nunawa mutanen Annabi Lut (a.s) yadda zasu rinka neman junansu.
A yau,an wayi gari duniyar kimiya da fasaha musamman duniyar gizo(internet) na daya daga cikin hanyoyin da ke koyarda wadannnan munanan dabi’u musamman a social media inda zaka tarar kala suna yi a 6oye yanzu sun fito a fili har groups su ke da shi daban daban a facebook,da whatsapp.Wani abin takaice sai ka tarar mafi yawansu duka Hausawa ne.Sharrin yahudawa ne kuma sannu a hankali suna samun nasara.

Wannan wata mummunar dabi’a ce dako dabbobi basa neman junansu sai gaya ta bayyana ga ‘yan adam.Allah ya la’ani mai yinta.Wanda duk Allah ya la’ana to wallahi ba shi ba albarka a rayuwarshi ba shi ba alhairi.

Mala’iku suna da hankali amma basu da sha’awa.
Mutane suna da sha’awa kuma suna da hankali.
Suko dabbobi suna da sha’awa amma basu da hankali.Anan,a duk sanda hankalin dan adam ya rinjayi sha’awarsa to sai ya koma daga cikin mala’iku domin suke da hankali amma basu da sha’awa.
Idan ko sha’awar Dan adam ta rinjayi hankalinsa to sai ya koma daga cikin dabbobi domin suke da sha’awa amma basu da hankali.

Masifa ce ta shigo a cikin al’umma wace zata iya haddasa kowane irin hushi na Ubangiji.A yau bala’ukkan da muke ji awasu kasashen waje na girgizar kasa,iska da tsawa gami da kashe kashe da yake yake ana zubarda jini ba kakkautawa gasu nan biye damu.

Ta fannin zamantakewa da kiwon lafiya a hakika akoi illoli masu yawa da madigo ke haifarwa jiki.

1.yana kauda sha’awar aure ga baki daya.Domin addinance akan daura aure tsakanin mace da namiji.To macen dake madigo zata kasance bata shawar namiji gabaki daya.ko tayi auren,tayi ne kawai amma ba zata ji shawar mijinta ba.

2.Ba zata sami biyan bukata a kwanciyar aure ba.Shi kuma jima’i a tsakani ma’aurata yana kara gina so da kauna a tsakanin juna.koda an sadu da ita to ba zata ji shawarta ta gushe ba har sai ta hadu da yar uwarta macce sun goga da juna.shi yasa kake ganin matan aure na aikata wannan mummunar dabiar.

3.Madigo na haifarda yaduwar ciwon sanyi.A duk sanda wacce take dauke da ciwon sanyi taiyi tarayya da wacce bata da shi to anan zai yadu.Domin wannan discharge din yana daukeda kwayoyin cuta da zai yadu ya shafeta.

4.Madigo yana haifarda cutukan da ke lailayi ga farjin mata.Idan mai kaikayin mara ko kuraje a cikin farji ko zubar farin ruwa sanadin wani infection kamar na vulvo vaginal candidiasis,yeast infection,da sauransu idan suka yi gogayya da juna to za a dauki wannan ciwon.

6.Yana haifarda yaduwar cutar tsida.kuma banga yanda za a kare wannan kwayar cutar ba domin takan biyo ruwan dake fitowa a gaban mace ta shafi yar uwarta kuma ba dan ayi amfani da condom ba.

8.Yana haifarda ciwon mara – Dama,su mata sun fi kowa yawan ciwon mara,wasu dai da shi aka haife su wasu kuma a lokacin al’ada wasu kuma daga baya suka dauko shi a wani guri,(infections).To gogayyar da suke yi gaba da gaba da juna na haifarda kamuwa da ciwon mara musamman na infections.Ayi ta faman neman magani a rasa sanin dalili.

8.yana haifarda ciwon ruhi – Anan shi ciwon ruhi bafa ciwo bane da zaki gani a zahiri,amma a hakika zaki ji alamunsa a gangar jikinki.Na farko dai zai busar da zuciyarki ya kasance baki shakku ko tinanin zaki iya mutuwa a kowane lokaci.

Sha’awarki zata gushe ta koma ga yan mata kawai.Da zaran kin ga mace mai girman kirji ko duwawu duk sai sha’awarta ta kama ki.
Komai nisan ki da ita zaki iya nemanta.Har ki tsufa zaki kasance kina ganin sha’awar mata yan uwanki.

10.Sirrance zai janyo maki dushewar farin jini a fuskar maza,sai kiga duk masoyanki matane,gaki kyakkyawa amma bamai so,basirarki tabi ta dushe,tinaninki ya sauya.watarana sai ki kasa dainawa.zuwa a gaba sai ya busarda ke ki rinka ramewa duk ni’imar jikinki ta mace ta gushe kibi ki bushe.

Leave your vote


Like it? Share with your friends!

-1
64 shares, -1 points

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.