Idan ni ne shugaban kasa zan kama Obasanjo a cewar Oshimhole


Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshimhole, ya ce zai kama tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da shine shugaban Najeriya.

Oshimhole ya shawarci shugaban kasa Muhammad Buhari da ya bincika ya kuma kama tsohon shugaban “idan ya aikata ko wane irin laifi.”

A cewar Jaridar Thisday, tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC, ya yi wannan furucin ranar Talata a wurin bikin da aka gudanar domin karrama iyalan Marigayi MKO Abiola.

Oshimhole ya ce “Yakamata a kama shi matukar ya aikata wani laifi, ya kama da yawa daga cikin mu idan muna murnar cif Gani Fawehinmi muna da kwararan dalilan yin haka. A dukkanin abubuwan da suka faru ba mu taba biyan Gani da Falana kudi ba, sun kare mu ne kyauta.

“Gani ba ya tare damu a yau, amma ruhinsa yana nan,Falana yana nan kuma nima ina tsaye ko shugaban kasar dake mulki a wancan lokacin yanzu yana korafin cewa ana nema a takura masa .Ya sha takura muni kuma yasa aka kama ni.

“Shi a tunaninsa ba za a iya kama shi ba.Idan da nine shugaban kasa da sai na kama shi dukkanin mu yan Najeriya ne, zan iya tunawa wata rana na fada masa ‘ shugaba Obasanjo mune muka sa ka zama shugaban kasa amma ba kai kasa na zama ɗan Najeriya ba.”

A yan kwanakin da suka wuce tsohon shugaban kasar ya zargi gwamnatin shugaba Muhammad Buhari da shirin kala masa sharri domin kama shi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like