Idan Buhari yana nan muna samun wuta tsawon sa’o’i 24 – al’ummar Daura


Shugabanni da suka fito daga kananan hukumomi 5 dake karkashin masarautar Daura sun bayyana cewa al’ummominsu na samun wuta ta tsawon sa’o’i 24 ne kadai a duk lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari yake gari.

Buhari yaje mahaifarsa Daura domin halartar bukukuwan Babbar Sallah.

A ya yin ziyarar Sun ya bawa shugaban kasar kana su ka jawo hankalinsa da ya magance matsalolin da suke addabar yankin.

“Duk lokacin da shugaban kasa yake nan muna samun wuta ta tsawon sa’o’i 24. Amma idan bayanan ba a kawo wutar akai-akai,” a cewar Muhammad Sale daya daga cikin shugabannin.

Da yake mayar da martani, Buhari ya ce ya shirya inganta rayuwar yan Najeriya tun da ya gamsu cewa an zabe shine saboda sanin kudurinsa.

Shi kuwa sarkin Daura,Umar Farouq kira ya yi ga yan Najeriya da su goyi bayan shugaban kasar domin shawon kan matsalolin da ake fama da su a yanzu.


Like it? Share with your friends!

-1
88 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like