Ibrahim Salisu: Dan Kwallo Mafi Tsada A Kano Da Aka Saya Naira 5,000


An gudanar da wani ciniki mafi tsada a Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu a Najeriya, inda Super Stars ta dauki Ibrahim Salisu Iriyos a matsayin mafi tsada a garin.

Super Stars mai buga rukuni na biyu a gasar hukumar kwallon kafa ta jihar Kano ta sayo Ibrahin Iriyos daga Aston Villa ta Gano kan kudi naira dubu biyar daidai da fam 10.86.

BBC HAUSA ta ruwaito Dan wasan mai cin kwallo shi da kansa ya yi sha’awar komawa Super Stars da murza leda ganin tana mataki na sama fiye da kungiyarsa ta Aston Villa Gano.

Hakan ya sa Iriyos kan je Super Stars atisaye a lokacin da kungiyarsa Aston Villa ke yin hutu, wanda hakan ya sa nan da nan aka amince da yadda yake taka leda aka kuma cimma matsaya a dauko shi.

Idin Gano shi ne shugaban Super Stars wanda ya je wajen kocin Aston Villa, Abba Alasan Isa wanda ake kira Abba Goma suka cimma matsaya kan farashin Ibrahim Iriyos.


Like it? Share with your friends!

-1
84 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like