Hukunci kan maharin shagunan Turkawa | Labarai | DWA wannan Juma’a, kotun ta zarta da hukuncin zaman gidan yari na shekaru tara da rabi kan mutumin da aka samu da laifin kassara kasuwancin wasu Turkawa mazauna Jamus. An kiyasta asara na euro miliyan hudu a sakamakon jerin hare-harensa.

Asali ma dai, kotu ta same shi da laifuka har ashirin da shida, ciki har da yunkurin kisan kai a sanadiyar wutan da ya taba cinna wa kan wani shagon wani dan asalin kasar Turkiyya da ke a jahar Baveriya da shirinsa kitsa kai hari kan ofishin jakadanci da wani masallaci na Turkawa da ke biranen Munich da Kolon, ya kuma ce yana shirin kai ma limamai hari, sai dai daga karshe ya ce, yayi nadama.

An gano yadda ya kwashi tsawon lokaci yana koyon yada ake hada abubuwan fashewa daga shafin intanet na mayakan Kungiyar IS, da ya ke amfani da su, kafin a watan Mayun bara, jami’an tsaro su yi nasarar cafke shi. Ba a yarda an bayyana sunan maharin da kuma asalinsa ba.
 
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.