Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Jihar Kano Ta Janye Gayyatar Da Ta Aika Wa Matan Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero Da Sauran Manyan Masarautar Kano


A ranar Alhamis ne hukumar karbar koke-koke da yaki sa rashawa ta jihar Kano ta janye gayyatar da ta yi wa matan Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero guda biyu, matar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da sauran manyan hakiman masarautar Kano.

A dangane da rahoton Prime Times News, sanarwar janye gayyatar ta fito daga wata takarda mai dauke da kwanan watan 20 ga watan Yuni, 2019, wadda darektan karbar koke-koken al’umma da shiga tsakani na hukumar, Malam Sani Tahir, ya sanya wa hannu a madadin shuguban hukumar, Muhyi Magaji.


Like it? Share with your friends!

2

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like