HUKUMAR TACE FINA-FINAI TA KAMA DARAKTAN KANNYWOOD SUNUSI OSCAR 442


Hukumar tace finafinai karkashin jagorancin Isma’ila Na’Abba Afakallahu, tana zargin Darakta Sunusi Oscar 442 da laifu kamar haka.

•Ya saki wakar Hasashe (wadda yanzu haka kusan shekarar ta hudu da fita) ba tare da satifijek ba, wanda shi Oscar musanta laifin a gaban Kuliya. Domin ya ce ba shi ne ke da ikon fitar waka ba. Shi darakta ne.

•Akwai wakar Garzali Miko da aka dora a *YouTube* kwana baya (a kalla wata guda da ya ya wuce) ita ma wai ba yi censoring ba. Har ila yau Oscar ya musanta laifin, domin ya ce shi ko YouTube channel ba shi da ita. Saboda haka laifin da ake tuhumarsa bai aikata ba.

Lauyan Oscar ya yi iya bakin kokarinsa domin Alkali ya bada beli, hakan bai samu saboda Alkali ya dage shari’ar zuwa 20 ga watan nan da muke ciki.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like