Hukumar NAFDAC ta lalata jabun magunguna na naira biliyan uku cikin shekara daya


Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa wato NAFDAC ta kwace tare da lalata magunguna marasa inganci da darajar su ta kai naira biliyan uku cikin shekara guda.

Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana haka jiya a Abuja ya yin bikin murnar cikarta shekara daya da kama aiki.

Magungunan marasa inganci sun hada da kayan abinci da kuma sauran kayayyakin da ba a tantance ingancinsu ba.

Farfesa Adeyeye ta ce dauke jami’an hukumar da aka yi daga tashoshin jiragen ruwa daga shekarar 2011 ya zuwa 2018 ya jawo kara ruruta wutar matsalar jabun magunguna inda hakan ke barazana ga lafiyar mutanen kasa baki daya.

Ta ce hukumar na shirin sayo kayan aiki na zamani domin sanya ido kan jabun magunguna a matakin shiya dama jihohi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like