Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Jihar Katsina Ta Sanar Da Kudin Kujerar Wannan Shekarar


Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina na Shaidawa Maniyyatan Aikin Hajjin Bana 2019 Cewa Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa NAHCON Ta Tsaida Naira 1.519.113,10k A Matsayin Kudin Kujerar Aikin Hajjin Bana A Jihar Katsina, Wanda Maigirma Gwamnan Alhaji Aminu Bello masari CFR Dallatun katsina Matawallen Hausa ya Amince a Bayyana Masu.

Don Haka Hukumar na kira ga Maniyyatan da Suka Fara Biyan Kudin Ajiya da Su yi Kokarin Kammalawa da Kuma Masu Niyyar Biyan Kudin a Matsayin Sabbin Alhazai da Su Biya Daga Yanzu Har Zuwa 31st May, 2019 in Allah ya Kaimu.

Daga Karshe Hukumar na kira ga Maniyyatan Da Su Tabbatar Suna Halartar Taron Bita Alhazai Wanda Hukumar Zata Fara Yi Nan Gaba Idan Allah ya Kaimu.


Like it? Share with your friends!

-2
104 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like