Hukumar DSS ta sako Sowore


Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sako, Omoyele Sowore jagoran kungiyar da ta shirya gangamin juyin juya hali da su ka yiwa lakabi da #RevolutionNow.

An saki Sowore ranar Talata bayan umarnin da ministan shari’a , Abubakar Malami ya bawa hukumar na sakin Sowore da Sambo Dasuki.

An kama Sowore ranar 3 ga watan Agusta gabanin zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a fadin kasa baki daya.

An sake shi na wucin gadi bayan da ya shafe kwanaki 124 a tsare amma aka sake kama shi da karfin tsiya a harabar kotun tarayya dake Abuja kasa da sa’o’i 24 bayan sakinsa.

A cikin sanarwar da ya fitar ta sakin Sowore da kuma tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, Malami ya ce ya dauki wannan mataki ne domin bin umarni kotu da girmama doka da oda.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like