Hoton matuka jirgin yan sanda da mayakan Ansaru suka raunata


Matuka jirgi biyu aka jikkata lokacin da wasu yan bindiga da ake zargin mayakan kungiyar Ansaru ce suka bude wuta kan jirgi mai saukar ungulu na yan sanda wanda ke tattara bayanan sirri a lokacin da jami’an tsaro suka farma sansanin mayakan kungiyar ranar Laraba a Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriya, Frank Mba ya ce mayakan sun yi amfani da bindigar kakkabo jiragen sama wajen kai wa jirgin hari.

Ya kara da cewa an samu nasarar kashe mayakan kungiyar 245.

Ga wasu hotunan yan sandan biyu da suka jikkata.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like