Hillary Clinton ta nemi Buhari ya kawo karshen kisan masu zanga-zangar EndSARS


Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka,Hillary Clinton tayi kira ga shugaban kasar Najeriya, Muhammad Buhari da ya kawo karshen kisan da ake yi wa masu zanga-zangar EndSARS a kasar.

Kiran nata na zuwa ne bayan da aka yi arangama da sojoji da masu zanga-zangar a wurin karbar kudaden masu amfani da titi dake Lekki a jihar Lagos.

Ana zargin jami’an soja da bude wuta kan masu zanga-zangar abin da ya kai ga asarar rayuka.

Wasu hotuna da aka rika yadawa a shafukan Facebook da Twitter sun nuna mutane a kwance cikin jini.

Clinton ta fadi haka ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter inda a ciki ta nemi Buhari da kuma hedkwatar tsaro ta Najeriya da su kawo karshen kashe-kashen.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. It’s a shame you don’t have a donate button! I’d without a doubt donate to this excellent blog!
    I guess for now i’ll settle for bookmarking and adding your RSS feed to my Google
    account. I look forward to brand new updates and will share
    this website with my Facebook group. Chat soon!

    my website xnxx