Hatsarin tirelolin shanu ya lakume rayukan mutane 5 a Adamawa


Hukumar Kiyaye Haɗura ta Najeriya (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutum biyar sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a Jilima da ke Ƙaramar Hukumar Mayo Belwa ta Jihar Adamawa.


Hatsarin na manyan tirelolin da ke dakon shanu biyu ya auku ne ranar Asabar a kan babban titin Mayo Belwa zuwa Ganye, yayin da motocin suka bar garin Ngurore zuwa cin kasuwar dabbobi a garin Ganye.


Kazalika, wasu mutum 32 sun ji munanan raunuka daga cikin 53 da lamarin ya rutsa da su, a cewar jami’in rundunar FRSC reshen Jihar Adamawa Aminu Ibrahim.


Wani da ya tsallake rijiya da baya ya alaƙanta aukuwar hatsaarin da tuƙin ganganci, inda ya ce direbobin biyu na “tsere ne domin nuna bajintarsu ta tuki”.


“Gudu da tuƙin ganganci ne suka haddasa hatsarin saboda fasinjojin motocin sun yi ta ziga direbobin tare da yi musu kirari don su yi gudu,” in ji Aminu Ibrahim.

Leave your vote


Like it? Share with your friends!

1
77 shares, 1 point
Comments are closed.

58 Comments

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg