Hatsarin mota ya rutsa da wani sanata kwana guda kafin zabe


Ahmed Ogembe, sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya a ranar Juma’a ya tsallake rijiya da baya bayan da hatsarin mota ya rutsa da shi akan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Sanatan na kan hanyarsa ta zuwa Okene gabanin zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya na ranar Asabar.

Duke Opeyemi,mai taimakawa sanatan kan harkokin sadarwa shine ya shedawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya haka a wata tattaunawa ta wayar tarho da kamfanin.

Ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 09 na safiyar ranar Juma’a a garin Gegu dake karamar hukumar Koton Karfe dake jihar.

Ogembe na neman a sake zabensa a karkashin inuwar jam’iyar PDP.

A cewar Opeyemi motar sulke da sanatan yake ciki ta hantsula da yawa ,amma sanatan da sauran mutanen da suke ciki sun tsira ba tare da sunji ciwo ba.

Sanatan ya godewa Allah bisa yadda ya tseratar da rayuwarsa shi da sauran mutanen da suke tare.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like