Hatsarin mota ya lakume rayukan mutane uku a jihar Bauchi


Wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar Bauchi zuwa Maiduguri ya lakume rayukan wasu mutane uku a ciki har da wani dalibin Jami’ar Jihar Bauchi dake Gadau.

Dalibin mai suna Ibrahim Muhammad Karamba tare da wasu mutane biyu na kan babur ne lokacin da suka yi tawo mu gama da wata mota kirar Hiace mai cin mutane 18 wacce akafi sani da Hummer.

Hatsarin ya faru ne a kauyen Tirwun Kajitu dake da tazarar kilomita hudu daga reshen jami’ar dake Bauchi.

Tuni aka gudanar da jana’izar marigayin a mahaifarsa dake Misau inda wasu daga cikin shugabannin jami’ar suka samu halarta.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like