Hari ya halaka mutane 13 a Burkina Faso | Labarai | DWTsageru masu kaifin kishin addinin Islama dauke da makamai sun halaka sojojin Burkina Faso hudu da fararen hula guda tara a wani harin kwanton bauna a yankin arewacin kasar. Wata sanarwa ta rundunar sojan kasar ta ce lamarin ya faru a wannan Alhamis da ta gabata.

Fararen hular da harin ya ritsa da su na cikin tawogar mayakan sa-kai da ke taimakon sojojin yaki da tsageru.

Tuni sojoji suka mayar da martani tare da halaka mutane 34.

Ita dai kasar Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka tana kasance tana fuskantar hare-hare kungiyoyin Musulmai masu ikirarin jihadi na Al-Ka’ida da IS tun shekara ta 2015.

A watan Janairu sojoji sun kwace madafun iko domin magance matsalar, amma tana ci gaba da faruwa a yankin arewacin kasar.

 
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg