Har yanzu nine dantakarar PDP -Abba Kabir Yusuf


Bayan hukuncin da wata kotu ta yanke a ranar Litinin da ya soke takarar,Engr.Abba Kabir Yusuf a matsayin dantakarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP dan takarar ya ce hukuncin bai shafi takararsa ba , batun tsakanin jam’iya ne da kuma mai kara inda ya ce tuni jam’iyar ta dauki matakin da ya dace na daukaka kara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar mai dauke da sahannun,Sunusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun dan takarar gwamnan.

A cewarsa dan takarar zai cigaba da yakin neman zabensa har ya zuwa ranar Alhamis kamar yadda dokar zabe ta shekarar 2010 ta tanada.

“Har yanzu Engr Abba Kabir shine ɗan takarar jam’iyar PDP a zaben 2019 da za ayi ranar Asabar 9 ga watan Maris.

“Hukuncin bashi da alaka da dantakarar jam’iyar, rikici ne na cikin gida da daya daga cikin yan takarar kuma tuni jam’iyar ta dauki matakin da ya dace,”a cewar sanarwar.

Har ila yau jam’iyar ta zargi jam’iyar APC mai mulki da hannu a batun

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like