Har yanzu ina takarar shugaban ƙasa – Fayose


Duk da cewa jam’iyar  PDP ta yanke hukuncin cewa dan takarar shugaban ƙasa karkashin tutar jam’iyar a zaben shekarar 2019 zai fito ne daga yankin arewacin ƙasarnan, gwamnan jihar Ekiti, Ayodele  Fayose  a ranar Juma’a yace bai janye ba daga takarar. 

Fayose yace ya yanke shawarar rage yaƙin neman zaɓensa ne saboda zaben gwamnan jihar Ekiti da ke tafe ranar 14 ga watan Yuli na wannan shekara inda yakara da cewa da zarar an kammala zaben zai cigaba da yaƙin neman zabensa.

Fayose wanda ya bigi kirji cewa  zai kayar da tsohon gwamnan Kayode Fayemi idan har an tsayar da shi takara karkashin jam’iyar APC.
Ya kuma kawar da fargabar da wasu yan takarar suka yi na kira da shugaban cin jam’iyar na ƙasa karkashin shugabancin Uche Secondus kan ya takawa gwamnan birki kan tsoma baki da yake a zaɓen cikin gida da za gudanar, gwamnan ya ƙara da cewa jihar bata da wata rawa da take takawa a boye a zaɓen.

Fayose ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa a gidan gwamnatin jihar da malaman makarantun firamare dana sakandaren gwamnati dake jihar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like