Har yanzu ina jam’iyar PDP -Aduda


Sanata daya tilo dake wakiltar mazabar birnin tarayya Abuja a majalisar dattawa, Philips Tanimu Aduda, yace yana nan cikin jam’iyar PDP.

Aduda lokacin da yakewa manema labarai jawabi a jiya ya shawarci magoya bayansa da suyi watsi da jita-jitar sauya shekarsa ya zuwa jam’iyar APC.

“Ina so na bayyana ƙarara cewa ban fita ba daga jam’iyar PDP ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai da kuma kafar sadarwar zamani suka rawaito.Ina nan a PDP babu abinda ya haɗa ni da APC,”ya ce.

Aduda wanda ya yi magana ta bakin, Abdulrahman Muhammad Takushara ,mai taimaka masa kan harkokin siyasa ya ce ya kasance mamba a jam’iyar PDP tun shekarar 2003 kuma bai ga dalilin da zai sa ya fita daga jam’iyar da tayi silarsa zuwa majalisar tarayya ba.

Mutane da dama sun riƙa yadawa a kafar sadarwar zamani musamman Facebook cewa sanatan ya sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC.


Like it? Share with your friends!

-2
82 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like