Har yanzu Gwamna El-Rufa’i na killace bai fito ba- Gwamnatin Kaduna


Hankalin gwamnatin jihar Kaduna ya zo kan wani Bidiyo da ake yaɗawa wadda ke nuna Gwamna Nasir Ahmad El-Rufa’i ke zirga zirga a kan wasu titunan cikin garin Kaduna domin tabbatar da al’umma sun bi dokar da aka saka.

Da haka ne gwamnatin ke sanar da al’umma cewa wannan Bidiyon an dauka ne a ranar Juma’a 27 ga watan Maris kwana daya kafin ya ke6e kansa.

A ranar Asabar 28 ga watan Maris, Malam Nasir ya fito ya yi wa duniya jawabin sakamakon gwajin da aka yi masa na cutar Korona Bairos kuma sakamakon ya nuna ya kamu da wannan cuta. Tun bayan wannan lokaci Gwamnan ya killace kansa kuma har yanzu ya na killace.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like