Halin Kaskanci Da Wulakanci Da Dan Arewa Ke Fuskanta A Kurkuku Saboda Ya Musuluntar Da Kirista Ya Aure Ta


A 2016 jaridun Kudancin Najeriya suka yi caa akan Matashin Musulmi daga jihar Kano Yunusa Dahiru Yellow akan zarginsa da sato Kirista Eshe Ururu daga jihar Bayelsa tare da Musuluntar da ita gami da aurenta.

An gurfanar da shi a gaban kotu ya musanta zargin da ake yi masa.

An garkame shi a kurkukun Bayelsa, wanda daga bisani wata babbar kotu a Yenegoa ta bayar da belinsa a bisa sharadin sa hannun wasu mutane da kuma tarar Naira Miliyan Uku.

Ya yi aure ya haifi ‘ya mace ya sanya mata sunan Fatima mahaifiyar Lauya Huwaila da ta tsaya masa.

Rabi’u Musa Kwankwaso ya saya masa sabon Babur din A Daidaita Sahu don ci gaba da sana’a.

Yellow Yace “Duk cikin ‘Yan fursunan da suke tsare shi kadai ne musulmi yace basa Barin sa yana sallah sai ranar juma’ah yace hatta abinci sai dai su bashi garin kwaki

1. Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Attajiri AA Rano da kuma Lauya Huwaila sune suka tsaya aka bayar da belinsa.

2. Bayan Wata biyar yana zuwa kotu ya Fuskanci matsananciyar rashin Lafiya da ta hana shi halartar zaman kotu.

3. Gwamnan Bayelsa, ‘Yan Majalisar dokokin jihar, ‘Yan wakilai na tarayya da Sanatoci zuwa manyan jihar sun yi masa taron dangi sai ya koma kurkuku.

4. An bar Lauya Huwaila ita kadai tana Fafutukar kare shi har abin ya fi karfinta.

5. Mahaifinsa ya Haifi ‘ya ya sa mata sunan Huwaila saboda jin Dadin abinda ta yi wa ‘yarsa.

6. Yunusa Yellow ya koma kurkukun Bayelsa inda ya koka yana fama da matsananciyar yunwa.

7. Mahaifinsa yayi kuka ya kara kuka ya sayar da gonarsa ya sayar da awakan gidansa ya rasa wayar da zai rika tuntubar mutane, ya sayar da injin ban ruwansa duk saboda a saki dansa.

8. Ko a kwannan nan da kyar ya hada Naira 500 ya Aikawa Yunusa zuwa Bayelsa.

9. Ya yi zirga-zirga zuwa birnin Kano ya fi sau 50 yana neman dauki kowa ya gudu ya kyale shi.

10. Ya nemi jagororin siyasar yankin su na Karamar Hukumar Kura kama daga Kansila, Dan majalisar jiha, Dan majalisar tarayya, Sanata, Shugaban Karamar Hukuma amma ba wanda ya kai masa dauki.

11. Shugaban Karamar Hukumar Kura, Hayatu Dorawar Sallau da Muntari Ciroma sun ce ba za su taimaka ba saboda shi ba dan siyasa ba ne.

Zuwa yanzu ana bukatar wasu kudade domin fito da belinsa wanda mutum daya zai iya biya daga cikin yan siyasa, masu mulki, attajirai da ‘yan kasuwar jihar Kano.

*Rabi’u Sadauki Kura na gidan Rediyon Rahma a jihar Kano ne yayi hira da mahaifin Yunusa Yellow.


Like it? Share with your friends!

-1
121 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like