HAJJIN BANA: An Jibge Mahajattana Katsina Ba Tare Da An Ba Su Masauki Da Kulawa Ba


Daya daga cikin mahajjatan wanda ya bayyanawa RARIYA halin da suke ciki, ya kara da cewa tun jiya aka jibge su a Makka bayan sun zo Umrah daga Madina, inda aka bar su babu ci kuma babu masauki. Sannan kuma sun nemi jami’an hukumar Alhazan reshan jihar Katsina sun rasa domin mika korafinsu.

Rashin masaukin ya sa dole Alhazan wadanda sun kai kusan su dari suka tare a masallaci, yayin da wasu kuma suke jibge a bainar jama’a.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like