Ma’aikatar cikin gidan kasar Haiti ta fidda sanarwar cewa, Claude Joseph da ke rike da mukamin Firaministan kasar na wucin gadi tun bayan kisar gilla da aka yi wa shugaban kasar Jovenel Moise zai mika mulkin ga abokin karawarsa Ariel Henry da ke samun goyon bayan kasashen ketare nan ba da jimawa ba.

Ana sa ran wannan sanarwa ta kawo karshen rikicin neman shugabanci da kasar ta Haiti ke ciki, musamman ma tsakanin wadannan mutanen biyu. Ariel Henry shi ne wanda marigayi shugaba Moise ya nada firaminista, kwanaki biyu kafin kisansa da ba a kai ga rantsar da shi ba.

Kasar ta Haiti dai na fama da tarin matsaloli ko baya ga rikicin siyasa, al’ummar kasar na fama da matsanancin talauci da tsadar rayuwa. ┬áHar kawo yanzu ana ci gaba da kame mutanen da ake tunanin suna da hannu a kisan shugaban kasar.