Hadiza Gabon Vs Amina Amal


Da farko dai ya kamata jama’a su sani, duk cikin bayanin da Amina Amal ta yi, babu inda ta ambaci sunan Hadiza Gabon, amma kuma ita Gabon din sai ta sha jinin jikinta ta ce da ita ta ke. To in ba rami me zai kawo maganar rami ?

Gaskiyar al’amari shi ne: dole jama’a su yarda babu karen da ba bule ba cikin wadannan jarumai biyu, in har Amina Amal ta karbi laifuffukanta na irin ‘barnar da ta ke, to wajibi ne ita ma Gabon ta yarda cewar ta na aikata abin da ta zargi kanta da shi.

Sannan kuma, a tsarin shari’a da doka, duk yadda mutum ya kai ka siffanta surarka wajen yi maka shagube da gugar zana ko danganta ka da wani laifi, babu abin da doka ta isa ta yi masa matukar bai fito ‘baro-baro ya kama sunanka ba. A nan babu inda Amal ta siffanta ko da kamannin gabon cikin kalamanta balle inda ta kama sunan Gabon. Amma duk da haka ta tsargu har ma ta yi mata titsiye gami da duka.

Kuma wannan ya isa ya ba wa ‘kungiyoyin kare hakkin mata da masu kare hakkin dan adam dama su bi wa Amal hakkinta domin abin da gabon ta yi mata cin zarafi ne da keta hakkin dan adam. Domin ko da sunanta ta kama cikin kalaman da ta yi, to ba ta da hurumin da za ta yi mata titsiye balle ta tilasta mata amsa laifi cikin duka da zagi. Kotu ce ta ke da hurumin tuhumarta. Ba shakka wannan danyen hukunci da Gabon ta yankewa Amal, ya ci karo da doka da kuma hakkin bil’adama.


Like it? Share with your friends!

1

You may also like