Gwamnonin PDP 6 sun gana da Wike


Gwamnoni shida da suka fito daga jam’iyyar PDP a ranar Juma’a sun gana da Nyesom Wike gwamnan jihar a gidan gwamnatin jihar dake Fatakwal.

Ganawar ta samu halartar gwamnan jihar Imo,Emeka Ihedioha, Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto,Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa,Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na jihar Benue da kuma na jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle.

Gwamnonin sun iso gidan gwamnatin jihar Rivers da misalin karfe 06:00 na yamma inda suka wuce kai tsaye sashen gidan gwamnan inda taron ya gudana cikin sirri.

Mai magana da yawun gwamnan,Simeon Nwakaudu ya tabbatar da ganawar sai dai bai yi karin haske ba.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like