Gwamnonin arewa za su zabi sabon shugaban a wurin taron da suka fara a Kaduna


Gwamnoni dake halartar taron ya yin da suka halarci sallar Juma’a

A ranar Juma’a ne gwamnonin arewa 19 za su zabi sabon shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa biyo bayan karewar wa’adin shugaban kungiyar, gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

Gwamnan jihar ta Borno da ya yiwa gwamnonin jawabi ya yin taron dake gudana gidan gwamnatin jihar Kaduna ya shawarci gwamnonin da suka halarci wurin taron da su goyi bayan duk wanda ya samu nasarar zama sabon shugaban kungiyar.

Shettima ya kuma nemi gafara daga abokan aikinsa idan har ya saba musu a lokacin da yake gudanar da aikinsa.

Shugaban mai barin gado ya lissafa nasarori da dama da kungiyar ta samu karkashin jagorancinsa inda ya shawarci shugaban da zai maye gurbinsa da ya kai kungiyar ya zasu mataki na gaba.

Duk da cewa shugaban bai bayyana yadda za a zabi sabon shugaban ya shawarci abokan aikinsa da su goyi bayan duk wanda aka zaba.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like