Gwamnonin Arewa Sun Tsayar Da Buhari A Matsayin Dan Takararsu A 2019A yau Juma’a ne, Gwamnonin jihohin Kaduna, Malam El Rufa’i, Kano, Umar Ganduje, Niger, Abubakar Sani, Adamawa, Jubrilla Bindow, Kogi, Yahaya Bello, Yobe, Ibrahim Geidam suka tsayar da Shugaba Muhammad Buhari a matsayin dan takarar Shugaban kasa a 2019.

Gwamnonin sun cimma wannan matsayin ne bayan sun halarci Sallar Juma’a da Buhari a fadarsa inda Gwamnan Kaduna, Malam El Rufa’i ya jaddada cewa Buhari dan Nijeriya ne kuma yana da ‘yancin sake tsayawa takara idan har yana sha’awar yin hakan.


Like it? Share with your friends!

-1
127 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like