Gwamnonin APC sun ziyarci Buhari a Daura


Shugaba kasa, Muhammad Buhari ya karbi bakuncin gwamnonin jam’iyar APC a gidansa dake Daura a cigaba da bukukuwan babbar Sallah.

Wasu daga cikin gwamnonin da suka kai ziyarar sun hada da, Kayode Fayemi na jihar Ekiti,Atiku Bagudu na jihar Kebbi,Babajide Sanwo-olu na jihar Legas da Godwin Obaseki na jihar Edo.

Har ila yau mataimakin shugaban majalisar dattawa,Ovie-Omo Agege, sakataren gwamnatin tarayya,Boss Mustapha, Ibrahim Magu shugaban EFCC da kuma Sheikh Ibrahim Ali Pantami na daga cikin wadanda suka gana da shugaban kasar a ranar Talata


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like