Gwamnonin APC 7 sun goyi bayan takarar Oshimhole


Gwamnoni bakwai na jam’iyar APC mai mulki da jagoran jam’iyar na kasa Bola Ahmad Tinubu da kuma shugaban jam’iyar na farko, Cif Bisi Akande sun kai ziyarar nuna goyon baya ofishin yakin neman zaben,Kwamared Adam Oshimhole, mutumin da yake kan gaba a neman takarar zama shugaban jam’iyar.

Gwamnonin da Oshimhole ya jagorance su suka zaga ganin ginin sakatariyar ofishin sun hada da Atiku Bagudu, na jihar Kebbi; Abdullahi Umar Ganduje, na jihar Kano; Tanko Alamkura, na jihar Nasarawa, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akerdelu; Tanko Al-makura na jihar Nasarawa; Simong Lalong, na jihar Plataeu; Ibikunle Amosun na jihar Ogun da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi.

Bagudu wanda ya yi magana da manema labarai ya bayyana cewa dukkanin gwamnonin suna farin ciki da takarar neman shugabancin jam’iyyar da tsohon gwamnan jihar Edo yake .

Ya ce kwarewar Oshimhole a matsayin tsohon gwamna, tsohon shugaban kungiyar kwadago dan fafutukar dimakwaradiya alamu ne dake nuna ingancinsa.

Ganduje ya ce kasancewar a wurin wata manuniya ce dake nuna cewa Oshimhole zai samu dukkanin kuri’ar wakilan jihar Kano.


Like it? Share with your friends!

-1
66 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like