Gwamnoni  sun goyi bayan ƙirƙiro ƴan sandan jihohi


Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce ƙirƙiro ƴan sandan jihohi zai tai maka wajen  maganin matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar nan.

 Da suke magana ranar Litinin a ƙarshen taron kasa kan harkar tsaro da majalisar dattawa ta shirya, Abdulaziz Yari, shugaban ƙungiyar yace ƙasarnan ba za a iya lura da ita ba daga Abuja.

Jawabin nasa na zuwa ne kwanaki uku bayan da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo yace ƴan sandan jihohi ita ce hanyar da yakamata abi.

“Yau muna kara jaddada kiran mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo da kuma matsayin taro kan harkar tsaro da muka gudanar  a watan Agusta, akwai bukatar yan sandan jihohi zamu iya cewa hakan ne kawai mafita,” ya ce.

Gwamnan ya cigaba da cewa kasa mai girman Najeriya baza a iya lura da harkar tsaron yan sandanta daga Abuja ba.

Yari ya ƙara da cewa jihohin da suke da sha’awa ne kawai ne za su iya ƙirƙiro ƴan sandan.


Like it? Share with your friends!

2
87 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like