Gwamnoni 12 ne za su jagoranci kwamitin shirya babban taron zabar shugabanni jam’iyyar APC na kasa


Jam’iyyar APC ta kafa wani kwamiti mai mambobi 68 da zai gudanar da babban taron zaben shugabannin jam’iyar da za a gudanar a cikin watan Yunin wannan shekarar.

Osita Izunaso, sakataren tsaren-tsaren jam’iyar na kasa shine ya bayyana haka cikin wata da ya fitar a yau Lahadi.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Badaru Abubakar, gwamnan jihar Jigawa, ya yin da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredelu zai kasance mataimakinsa sai kuma,Ben Uwajumogu a matsayin sakatare.

Har ila yau kwamitin ya kunshi gwamnonin APC goma, Rochas Okorocha (Imo) Kashim Shettima (Borno) Aminu Bello Masari (Katsina), Ibrahim Geidam (Yobe) da Abiola Ajimobi.

Sauran sune Nasiru El-Rufai (Kaduna), Simon Lalong (Plateau), Bindow Jibril (Adamawa), Yahaya Bello (Kogi) da kuma Godwin Obaseki (Edo).

Har ila yau kwamitin na dauke da sunayen wasu sanatoci da suka haɗa da Ahmad Sani Yerima, Adamu Aliero, Danjuma Goje, Abdullahi Adamu, George Akume, Ovie Omo-Agege, Andrew Uchendu, Abdullahi Danbaba, Baba Kuka da kuma John Enoh.

Tun da farko yinkurin tsawaita wa’adin mulkin shugabannin jihar ya gamu da turjiya daga wurin jagoran jam’iyar na kasa, Bola Ahmad Tinubu da kuma shugaban kasa Muhammad.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like